Search
Close this search box.

Sojojin HKI Sun Kai Hare Hare A Kan Wani Gini A Kudancin Birnin Beirut A Yau Jumma’a

A dai dai lokacinda kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cilla makaman roka kimani 150 daga jiya Alhamis zuwa yau Jumma’a a kan

A dai dai lokacinda kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cilla makaman roka kimani 150 daga jiya Alhamis zuwa yau Jumma’a a kan wurare daban daban a kan arewacin HKI, dazo da rana ne kafafen yada labaran HKI suka bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hari kan wani gina a kudancin birnin Beirut na kasar Lebanbon inda ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 3.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kafafen yada labaran yahudawan sun bayyana cewa jirgin yakin samfurin F- 15 ne ya kai hare haren na birnin Beirut.

A dayan bangaren kuma kungiyar Hizbullah ta kara yawan makamai masu linzami wadanda take cillawa kan matsugunan yahudawa a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Labarin ya kara da cewa an ji kakar jiniyar hatsurra na ta tashi a matsugunan yahudawa da dama wadanda suka hada da garin Jalil a arewacin kasar Falasdinu da aka mamamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments