Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kutsawa cikin yankunan Quneitra na kasar Siriya
Gidan talabijin na kasar Siriya ya watsa rahoton cewa: Bayan kara mamaye wasu yankunan da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a kasar Siriya, a halin yanzu sun fara kutsawa cikin garin Suwaya da ke yankin Quneitra da ke kudu maso yammacin kasar Siriya.
Majiyoyin sun kuma bayyana cewa: Motocin bulldozer da tankokin yakin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun shiga yankin madatsar ruwan Mantara da ke lardin Quneitra, kuma sojojin mamaya sun kafa wuraren binciken soji tare da kafa shingaye a kusa da madatsar ruwan.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta ce: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kutsa kusan kilomita 7 a cikin yankin kasar Siriya da ke tsakanin Siriya da haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma ta sanar da mutanen kauyukan Umm al-Azam da al-Adnaniyya lokuta na musamman na shiga da fice a yankin.
Kamar yadda a jiya Talata, motocin masu sulke na haramtacciyar kasar Isra’ila tare da rakiyar sojoji, suka shiga cikin tsaunukan Sharat al-Harmon, inda suka kafa wani sabon matsayi a kan tsaunin da ke kallon yankin kudu maso yammacin birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya.