Sojojin gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa
Sojojin gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 268 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama, da kuma harba makamai masu linzami, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da aka shiga mummunan yanayin jin kai sakamakon killace yankin da suka yi, bayan ga gudun hijirar da al’ummar yankin fiye da kashi 95% suka yi.
Wakilan Cibiyar Yada Labarai ta Falasdinu sun ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya da manyan bindigogi sun ci gaba da kai munanan hare-hare a jiya Lahadi a sassa daban-daban na Zirin Gaza, inda suka kai hari kan gidaje da wuraren taruwan ‘yan gudun hijira da kan tituna, inda suka kashe Falasdinawa masu yawa tare da jikkata wasu na daban.
Tun a ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata ne sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da sintiri a wasu manyan unguwanni a birnin Rafah, inda suka shiga unguwar Shuja’iya a rana ta hudu a cikin halin luguden bama-bamai ta sama da na bindigogi tare da yin mumunan kisan kiyashi, yayin da masifar yunwa ta kara kamari a arewacin Zirin Gaza tare da ci gaba da hana shigar da kayan agaji da kuma raguwar kayyakin bukatu a kasuwanni.