Search
Close this search box.

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-Hare Kan Garuruwan Falasdinawa

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai jerin hare-hare kan yankunan Gaza, Rafah da Deir al-Balah da suka yi sanadin shahadar Falasdinawa da jikkatan wasu na

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai jerin hare-hare kan yankunan Gaza, Rafah da Deir al-Balah da suka yi sanadin shahadar Falasdinawa da jikkatan wasu na daban

A hare-haren wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan yankuna daban-daban na Falasdinawa ta hanyar jiragen saman yaki a yau Talata sun yi sanadiyyar shahadar Falasdina masu yawa tare da jikkatan wasu na daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Dangane da abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a rana ta 277 da aka kwashe ana kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, hare-haren a yau ma sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu na daban sakamakon hare-haren jiragen saman sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila musamman kan wani gida a birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza.

Haka nan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi luguden wuta kan yankunan da suke shiyar yammacin birnin Rafah, tare da kai farmaki a kusa da cibiyar kula da lafiya ta Shifa da ke yammacin birnin Gaza da kuma wata makaranta a Nuseirat.

Majiyoyin lafiya a asibitin Baptist sun ruwaito cewa sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun tilastawa kungiyoyin likitoci rufe asibitin bayan da suka killace shi tare da yin harbe-harbe a cikin harabarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments