Sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila Sun Gudanar Da Mummunan Samame A Yankunan Falasdinawa

Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun kaddamar da wani gagarumin samame a kauyuka da garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan Rahotonni sun bayyana yadda sojojin

Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya sun kaddamar da wani gagarumin samame a kauyuka da garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan

Rahotonni sun bayyana yadda sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da kai hare-hare da farmaki kan sassa daban-daban da suke yankunan yammacin kogin Jordan, inda samamen suka shafi garuruwan Nablus, Ramallah, Tulkaram da Khalil, baya ga wasu kauyuka masu yawa da suka hada da kama Falasdinawa da kuma fuskantar arangama da ‘yan gwagwarmaya.

Kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Wani matashi ya ji rauni sakamakon harsasai da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka harbe shi da su a garin Ramallah, kuma wata babbar gobara ta tashi a wata kasuwar kayan lambu da ke tsakiyar birnin, sakamakon fashewar bama-bamai da iskar gas da sojojin yahudawan sahayoniyya suka harba kan kasuwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments