Sojin Yamen Sun Bayyana Inda Zasu Kai Hari A kamfanin Aramco

sojojin kasar Yamen sun sha alwashin kaddamar da hari a kamfanin mai na Aramco amtsayin mayar da martani

Dakarun sojin kasar yamen sun fitar da sanarwar gaggawa ga dukkan fararen hula da sauran ma’aikata da su janye jikinsu daga kusa da kamfanin mai na Aramco na kasar saudiya , sun kara da cewa muhimman wurare a kamfanin na Aramco suna daga cikin halastattun wuraren da zasu kai hari.

A cikin jerangiyar bayanai da suka fitar a yau latala, kakakin sojon kasar yamen birgediya Janaral Yahya Saree ya bayyana cewa dakarun kasar yamen sun yi gargadi game da hare haren mayar da martani da za su kai kan  kasar Saudiya saboda harin da take kai musu.

Haka zalika dakarun sojin kasar yamen sun gargadi dukkan fararen hula da ma’aikata dake zaune a kusa da kamfanin mai na Aramco da su bar wajen cikin gaggawa, saboda  suna daga cikin wuraren da zasu kai  hari, yace  gaggauta tserewa daga wajen zai tseratar da rayukan fararen hula.

Wannan sanarwar gaggawar ta zo ne bayan barazanar da kakakin sojan hadin guiwa na amurka da saudiya yayi na cewa fararen hula su fice daga yankunan dake kusa da birnin sana’a

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted