Rundunar Sojin Mali (FAMa) ta sanar da cewa ta sake kwace ikon yankin Anefis bayan kwanaki da dama tana fafatawa da kungiyoyin JNIM da (Azawad Liberation Front) a arewacin kasar.
A cikin wata sanarwa, Babban Hafsan Sojojin Mali ya tabbatar da cewa Rundunar Sojin Mali (FAMa) ta sake samun cikakken iko a yankin.
An kaddamar da ayyukan ne da nufin kare yankin daga barazanar ta mai ikirari da sunan jihadi (JNIM) da kuma kungiyar ‘yan tawayen FLA.
Rundunar Sojojin Mali (FAMa) ta ce an kwato Anéfis tare da goyon bayan Rundunar Sojojin Afirka ta Ma’aikatar Tsaro ta Rasha da kuma rundunar hadin gwiwa ta GATIA da MSA.
An yi nasarar kwato yankin da aka yi wa kawanya tare da fatatakar kungiyoyin masu dauke da makamai daga garin.
Rundunar Sojojin Afirka ta kuma bayar da rahoton cewa babu wani asarar rai da aka samu a tsakanin rundunoninta a lokacin fafatawar.
Yankin Anéfis, wanda ya hada Gao, Kidal, da Aguelhok, ya kasance muhimmiyar cibiyar sojoji a arewacin Mali.
Wadannan ci gaban sun zo ne bayan hare-hare da aka kai a ranar 4 ga Yuli kan wasu yankuna na Mali, ciki har da Anéfis, Gao, Sévaré, Aguelhok, da Kéniéroba.
A cewar hukumomin Mali, sake kwace Anéfis ya zama wani sabon mataki a ayyukan da aka gudanar tun farkon wannan farmaki.