Sojin Mali Sun Cafke Wasu Muggan ‘Yan Ta’adda

Rundunar Sojin Mali ta sanar da cewa dakarunta sun kama wasu mutum biyu, inda daya daga cikinsu jagora ne a wata kungiyar ‘yan ta’adda a

Rundunar Sojin Mali ta sanar da cewa dakarunta sun kama wasu mutum biyu, inda daya daga cikinsu jagora ne a wata kungiyar ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa ta kama “Mahamad Ould Erkehile wanda aka fi sani da Abu Rakia”, da kuma “Abu Hash” wanda suka ce shi ne ke jagorantar kungiyar.

Rundunar ta kuma ce ta kashe ‘yan ta’adda da dama a lokacin wani samame data kai a arewacin kasar.

Sojojin na zarginsa da kitsa muggan hare-hare a yankunan Menaka da Gao da ke arewa maso gabashin kasar, da kuma hare-hare kan sojojin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments