Mayakan Yamen Sun Kai Hari Kan Matatar Mai A Saudiya

dakarun sojan kasar yamen sun kai hari kan mamatar mai a kasar saudiya da makamai masu linzami

Brigediya Janaral Yayha saree kakakin rundunar sojin kasar yamen ya sanar cewa dakarun sojin yaman sun kaddamar hari kan kamfanin mai na Ras tanura dake gabashin kasar saudiya , yace harin ya sauka a inda akai nufi, kuma ya jawo tashin gobara a muhimman kayayyaki dake wajen

A cikin bayani da ya fitar a yau talata Yahya Saree ya kara fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa a wani hari na daban da dakarun kasar yamen suka kai, sun hari wasu motocin soji guda biyu na kasar saudiya da makami mai linzami,

Haka zalika sun kakkabo wani jirgin sama a filin saukar jiragen sama na Najran da kuma wasu a sansanin soji na sarki khalid dake khamis mushait, kuma dukkan makamai masu linzami da aka harba sun fada a inda aka nufa

Sanarwar baya bayan nan ta zo ne bayan musayar wuta da aka yi tsakanin kasar yamen da saudiya , inda dakarun sojin yamen suka sanar da kai hare haren mayar da martani da makamai masu linzami da jiragen marasa matuki kan sansanin sojin kasar saudiya da bangaren makamashi a Riyadh da Yanbu da kuma rabigh

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted