Tsibiran da sojojin na Sudan su ka shimfida ikons a cikinsu suna a cikin tekun “Red Sea” ne,bayan da su ka kori mayakan rundunar “Kai Daukin Gaggawa” a karkashin Hamidati.
Haka nan kuma sun shimfida ikonsu akan wasu sansanonin soja da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gina a cikin wadannan tsibiran, tare da hadin gwiwar HKI
Bugu da kari rahotannin sun ambaci cewa; sojojin na Sudan sun kama mayakan na rundunar kai daukin “Gaggawa” da dama, tare da wasu jami’an kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Gwamnatin kasar Sudan ta soja ta sha zargin kasashen waje da su ka hada da HDL da cewa suna taimakawa rundunar kai daukin gaggawa da kayan yaki. Haka nan kuma tana zargin kasar da satar arzkinin gwal na kasar ta Sudan.