Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin

A wata tattaunawa ta wayar tarho, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yankin tare da jaddada muhimmancin hana ayyukan da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin. A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar […]

Iran ta bayyana kudurinta na mayar da martani ga ta’addancin Isra’ila

Iran ta ce ta kuduri aniyar mayar da martani ga matakin wuce gona da iri da Isra’ila ta dauka kan kasar a baya-bayan nan, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta a wannan bangare ba. “Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na mayar da martani kan  gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba, Wannan […]

Afirka ta Kudu za ta mika takardar shaidar kisan kiyashin Isra’ila a  Gaza ga ICJ

A wannan Litinin ce kasar Afrika ta kudu ke shigar da wani cikakken bayani akan “Isra’ila” a gaban kotun kasa da kasa (ICJ) wanda zai kara karfafa hujjar cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Falasdinu. Wata majiyar ofishin jakadancin Afirka ta Kudu da ba a bayyana sunanta ba ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na […]

Hezbollah ta kai hari kan kamfanin kera kayan soji na “Yodifat” na Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta Labanon na ci gaba da gudanar da wasu ayyuka na musamman da kuma kai farmaki kan yankunan arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye, a daidai lokacin da ta sanar da kaddamar da farmaki kan kamfanin kera makamai da kayan soji na “Yodevat” da ke kudu maso gabashin birnin Akka. […]

Sojan Ruwan Sudan Sun Shimfida Ikonsu Akan Wasu Tsibirai Na Kasar

Tsibiran da sojojin na Sudan su ka shimfida ikons a cikinsu suna a cikin tekun “Red Sea” ne,bayan da su ka kori mayakan rundunar “Kai Daukin Gaggawa” a karkashin Hamidati. Haka nan kuma sun shimfida ikonsu akan wasu sansanonin soja da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gina a cikin wadannan tsibiran, tare da hadin gwiwar HKI […]

Mayakan Hizbullah Suna Cigaba Da Kai Hare-hare A Kan Sojojin Mamayar HKI

Makayan na Hizbullah sun sanar da cewa, sun kai hari akan sojojin mamaya dake kusa da “Babu Fatima” wanda ke yankin Kafar-Kila, haka nan kuma a Aytarun. Hare-haren na kungiyar Hizbullah sun  yi sanadiyyar jikkata da kashe sojojin mamaya. Bugu da kari, mayakan na Hizbullah sun harba makamai masu linzami a cikin Falasdinu dake karkashin […]

Fiye Da Falasdinawa 1000 Ne Su Ka Yi Shahada  A Cikin Kwanaki 22

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 387,sojojin mamayar HKI suna cigaba da tafka laifukan yaki,inda a cikin kwanaki 22 ta kashe Falasdinawa 1000. Bugu da kari a wannan tsakanin sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 182,kamar yadda jami’in hukumar agaji a Gaza Muhammad Basal ya bayyana. A cikin kisan kiyashi na […]

Pakitsan: Isra’ila Barazana Ce Ga Zaman Lafiya Da Tsaron Yanki Da Duniya

Kakakin majalisar kasar Pakistan Sardar Ayaz Sadiq ya bayyana cewa; Kasarsa tana yin tir da harin da Isra’ila ta kai wa Iran, kuma yana cin karo da dokokin kasa da kasa. Kakakin  Majalisar dokokin kasar ta Pakistan ya kuma ce; Cigaba kai wa kasashe hare-hare da Isra’ila take yi, yana a matsayin barazana ga zaman […]

Kwamitin Sulhu Na MDD, Zai Yi Taron Gaggawa Bisa Bukatar Iran

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gana cikin gaggawa a wannan Litinin domin tattauna halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya. Kwamitin zai gana cikin gaggawa bisa bukatar Iran domin tattauna halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda fadar shugaban kasar Switzerland ta sanar. Kasashen Aljeriya, China da […]

Masar Ta Gabatar Da Bukatar Tsagaita Ta Kwanaki Biyu A Gaza

Shugaban Masar Abdel Fattah al Sissi ya bayyana cewa, kasar ta ba da shawarar tsagaita bude wuta na kwanaki biyu a zirin Gaza wanda zai kunshi musayar fursunonin Isra’ila hudu da aka yi garkuwa da su. Al Sissi wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a birnin Alkahira ya kara da cewa, za […]

Hare-haren Isra’ila Sun Yi Ajalin Falasdinawa 53 A Gaza Da Kuma 21 A Lebanon

Sojojin Isra’ila sun kashe akalla mutane 53 a Gaza da kuma wasu 21 a Lebanon a ranar Lahadi, yayin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana kaduwarsa kan “mummunan yanayin da ake ciki. Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a kudancin kasar Lebanon, a cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon. Akalla mutane […]

Lebanon Ta Bukaci Kwamitin Sulhu, Ya yi Allah-wadai Da Hare-haren Isra’ila

Kasar Lebanon ta ce ta mika koke ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda ta bukaci da a yi Allah-wadai da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi kan kasar Larabawar tare da yin kira ga kasashen duniya da su dorawa gwamnatin mamayar alhakin laifukan da ta aikata. Ma’aikatar harkokin wajen kasar […]

Hizbullah Ta kashe sojojin Isra’ila 5 a kudancin Lebanon

Isra’ila ta sanar a ranar Lahadin da mutuwar sojojinta 5 da ke cikin bataliya ta 8207 na Alon Brigade a yayin gwabza fada a kudancin Lebanon. Wannan ya sanya adadin sojojin Isra’ila da suka mutu zuwa 37 a kudancin Lebanon tun bayan fara mamayar kasa a ranar 30 ga watan Satumba. Kafafen yada labaran Isra’ila […]