Majiyoyin kasar Siriya sun ce an kashe ‘yan ta’addar da ke samun goyon bayan kasashen waje kusan 2,000 a yankin arewacin kasar a cikin makon da ya gabata a hare-haren hadin gwiwa da sojojin Siriya da Rasha suka kai.
Cibiyar hadaka ta kasar Rasha a Syria ta sanar da cewa, an samu mace-mace na baya bayan nan bayan hare-haren sun afkawa wuraren taruwa da maboyar ‘yan ta’adda a arewacin kasar, inda suka kashe ‘yan ta’adda kusan 120.
Wadanda suka mutun dai sun hada da wadanda aka kashe a yayin wani kazamin farmakin da aka kai musu a wajen taronsu a birnin Hama, inda aka ce ana gwabza fada a arewa maso yammacin birnin.
Tun da farko dai an bayyana cewa sojojin kasar Siriya sun kaddamar da wasu jerin hare-hare cikin nasara a arewacin Hama, inda suka fadada kewayen birnin da nisan kilomita 20.
Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar ‘yan ta’adda 300 na kungiyar ta’addancin nan ta Hayat Tahrir al-Sham (HTS) da suka hada da mayakan kasashen waje da dama.
Sojojin sun kuma lalata jiragen sama marasa matuka guda 25 na ‘yan ta’adda a arewacin Hama, baya ga yanke musu muhimman hanyoyin samar da kayayyaki.