Siriya Ta Ce Tawagar IAEA Zata Ziyarci Kasar

Hukumar makamashin Nukliya na kasar Siriya ta bada sanarwan cewa wata tawagar IAEA zata ziyarci kasar nan gaba kadan saboda bayyana wata sanarwa mai muhimmanci

Hukumar makamashin Nukliya na kasar Siriya ta bada sanarwan cewa wata tawagar IAEA zata ziyarci kasar nan gaba kadan saboda bayyana wata sanarwa mai muhimmanci dangane da cibiyar makamashin nukliya na kasar da ke Calandistine.

Shafin labarai na yanar gizo, Axios ya bada labarin haka a ranar litinin, ya kuma kara da cewa tawagar zata dauke dukkan makamashin nukliya da suke cikin cibiyar.

Cibiyar Al-Kabar ko calandistine dai wani shirin makashin Nukliya ne wanda gwamnatin Siriya ta yanzu ta gada, daga gwamnatin Asad. Kuma wannan cibiyar da kuma shirin kasar na makaman guba duk sun zama cikas wajen samun taimakon kasashen yamma don sake gina kasar Siriya kamar yanda suke fada.

Zuwan tawagar IAEA zai kawo karshen samuwar makamashin nukliya a kasar Siriya duk da cewa sojojin yahudawan sun lalatasu tun bayan faduwar Asad.

Kasashen yamma sun sanyawa sabuwar gwamnatin kasar Siriya sharadin ta rufe batun wadan nan al-amura guda biyu kafin su bada dama ko su taimaka a sake gina kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted