Search
Close this search box.

Shugabannin Kungiyoyin Gwagwarmaya A Gabas Ta Tsakiya Sun Gana A Tehran

Manyan kusoshi da shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya daban-daban na yankin gabas ta tsakiya sun gana a birnin Tehran babban birnin kasar Iran, tare da manyan kwamandojin

Manyan kusoshi da shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya daban-daban na yankin gabas ta tsakiya sun gana a birnin Tehran babban birnin kasar Iran, tare da manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).

Taron ya gudana ne a birnin Tehran a ranar Larabar da ta gabata tare da babban kwamandan IRGC, Manjo Janar Hossein Salami da kwamandan rundunar Quds, Birgediya Janar Esmail Qa’ani.

Haka nan kuma taron ya samu halartar  mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas Ismail Haniyeh, mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Jihad Islami Muhammad al-Hindi, da kuma wakilin gwamnatin ceton kasa ta Yemen, Mohammed Abdul-Salam.

Mahalarta taron sun tattauna kan halin da ake ciki a baya-bayan nan kan batutuwan siyasa, tsaro a yankinda, da kuma halin da ake ciki a yankin zirin Gaza, wanda ke fama da yakin kare dangi tun a watan Oktoban da ya gabata, da kuma ci gaba da taimaka ma Falastinawa da kungiyoyin gwagwarmayar Gaza suke yi, wanda ya biyo bayan farmakin Isra’ila a Gaza da kuma kisan kare dangi da take yi wa al’ummar yankin.

 Har ila yau, mahalarta taron sun jaddada bukatar ci gaba da fafutuka daga bangaren kungiyoyin Palastinawa da kuma ‘yan uwansu ‘yan gwagwarmaya a fadin yankin har sai an cimma “cikakkiyar nasara” kan ‘yan mamaya.

Kungiyoyin gwagwarmaya na yankin da suka fito daga kasashen Lebanon, Yemen, da Iraki suna ci gaba da kai hare-hare a kan sojojin yahudawan sahyuniya a cikin Falastinu da suka mamaye.

Shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya sun je Tehran ne domin halartar janazar marigayi shugaba Ibrahim Raeisi da mukarrabansa, wadanda suka yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na baya-bayan nan a arewa maso yammacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments