Shugabannin kasashen Iran da Siriya sun tattauna batun hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fagen yaki da ta’addanci
Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya zanta da takwaransa na kasar Iran Masoud Pezeshkian ta wayar tarho, inda suka tattauna batutuwan baya-bayan nan da suke faruwa a Siriya da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fagen yaki da ta’addanci.
A yayin wannan tattaunawa, shugaba Al-Assad ya jaddada cewa: Ta’addancin da ke faruwa yana nuni da manufofin da ba su dace ba na kokarin raba kan kasashen yankin da wargaza kasashen da kuma sake zana taswirori bisa muradun Amurka da kasashen yammacin duniya.
Al-Assad ya jaddada cewa: Wannan ta’addancin ba zai kara wa kasar Siriya da sojojinta komai ba, sai azamar dagewa a kan ci gaba da arangama da ‘yan ta’adda domin kawar da tushen ta’addanci a fadin kasar ta Siriya.
A nasa bangaren, shugaba Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Iran ta yi watsi da duk wani yunkuri na kawo cikas ga hadin kai da zaman lafiyar kasar Siriya, bisa la’akari da cewa cutar da hadin kan kasar Siriya tamkar wani rauni ne ga yankin, kwanciyar hankali da hadin kan kasashensu.
Haka nan kuma ya yi nuni da cewa: Muradin yahudawan sahayoniyya da Amurka a fili yake wajen kai hari kan kasashe da al’ummomin yankin, kuma abin da ke faruwa a kasar Siriya wani bangare ne na wannan buri, yana mai jaddada cewa Iran a shirye take ta ba da dukkan wani nau’i na goyon baya ga kasar Siriya domin kawar da ta’addanci da dakile manufofin masu gudanar da shi da magoya masa baya.