Shugabannin kasashen duniya suna ci gaba da mika ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Iran dangane da shahadar shugaba Ebrahim Raeisi a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar.
Raeisi ya rasu ne tare da tawagarsa da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, bayan da jirginsu ya fadi a dajin Dizmar da ke lardin Azarbaijan a ranar Lahadi.
Bayan bincike na tsawon sa’o’i da aka kwashe ana fuskantar cikas sakamakon rashin kyawun yanayi, masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin da ya fadi tare da tabbatar da mutuwar fasinjojinsa.
Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya ce ya yi matukar bakin ciki da kaduwa da wannan mummunan rashi na shugaban na Iran.
Ya kara da cewa “Ina mika ta’aziyyata ga iyalansa da kuma al’ummar Iran, in ji shi a wani sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Litinin.
Ministan harkokin wajen Indiya S. Jaishankar shi ma ya wallafa a shafin X cewa ya yi matukar kaduwa da jin labarin rasuwar shugaba Raeisi da takwaransa Hossein Amir-Abdollahian.
Shugabannin kasashen duniya da manyan mutane daga ko’ina cikin fadin duniya suna ci gaba da aikewa da sakon ta’aziyya zuwa ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, da alummar kasar kan wanann babban rashi.