Shugaban kasar Somaliya ya yi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan amincewa da yankin Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kan ta.
A yayin taron Doha, shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya yi magana kan halin da ake ciki a Gaza, yayin da kuma ya soki amincewa da ‘yancin kai na yankin ‘yan awaren Somaliland.
“Abin da muka gani da idanunmu a Gaza wani mataki ne na rashin tausayi a tarihin duniya” in ji Hassan Sheikh Mohamud, shugaban Somaliya.
Wannan bayanin ya zo ne yayin da Somaliya da Isra’ila ke cikin takun-tsaka tun bayan da gwamnatin Tel-Aviv ta kasance ta farko da amincewa da yankin a matsayin kasa mai cin gashin kan ta.
Gwamatin Mogadishu na mai bayyana matakin na Isra’ila a matsayin take hakkinta.
” Wannan ya sabawa dokokin kasa da kasa da wargaza kwanciyar hankali, tsaro, da ciniki ta hanyar da ta shafi yankin Afirka, Tekun yankin, da sauran duniya,” in ji shugaban Somaliya.
Somaliland ta ayyana ‘yancin kanta daga Somaliya a shekarar 1991, a lokacin wani rikici da ke ci gaba da kawo cikas ga zaman lafiyar wannan kasa ta Gabashin Afirka, kuma Isra’ila ita ce kasa ta farko da ta amince da wannan ‘yancin kai.