Pezeshkiyan Ya Dawo Gida Daga Taron Muhalli A Armenia

Shugaban kasar ta Iran da dawo gida da marecen jiya Juma'a bayan da ya halarci taron kasa da kasa na 17 akan kare tsarin halitta
shugaban kasar Iran

Shugaban kasar ta Iran da dawo gida da marecen jiya Juma’a bayan da ya halarci taron kasa da kasa na 17 akan kare tsarin halitta mabanbanta.

A jawabin da ya yi a wajen taron na birnin Yerevan, shugaban kasar ta Iran ya bayyana cewa; Barazanar yaki ba ta tsaya a akan bil’adama da kuma rusa muhimman cibiyoyi ba, wani makami ne a hannun bil’adama da yake rusa dabi’a da shi.

Haka nan kuma ya ce; Yaki yana kona da lalata dajuka, da kuma barnata kasa mai albarka da gurbata ruwa da tarwatsa dabbobi daga matsuguninsu na dabi’a.

Shugaban kasar ta Iran ta kuma ce; Yin aikin hadin gwiwa a tsakanin al’ummu a fagen kare muhalli yana da muhimmanci, kuma kare muhallin zai iya zama daya daga cikin hanyoyin diplomasiyya na zaman lafiya.

A gefen wannan taron, an yi ganawa a tsakanin shugaban kasar Iran da kuma fira Ministan kasar Armenia Nikol Vovayi Pashinyan. Bangarorin biyu sun yi tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.

Bugu da kari shugaban kasar ta Iran ta kuma gana da Fira ministan kasar Goergia Irakli Kobakhidze da bangarorin biyu su ka tattauna batutuwan da kasashen biyu su ka yi tarayya akansu.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted