Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba
Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka bayyana a matsayin haramtacciyar hanya sakamakon daukar matakin sake dawo da takunkuman da kasashen Turai uku suka yi kan Iran.
Qalibaf ya yi bayanin cewa: Share fagen hanyar da za a bi wajen sake kakaba takunkuman da kasashen Turai uku suka yi da kuma mayar da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran, ba bisa ka’ida ba ne, yana mai jaddada cewa, a hukumance kasashen Rasha da China sun fayyace cewa wadannan kudurorin ba su tilasta wa wata kasa aiwatar da su ba.
Ya kara da cewa Iran a nata bangaren, “ba ta daukar kanta cewa wajibi ne” ta dakatar da sarrafa sinadarin Uranium ko kuma ta mutunta duk wani daga cikin wadannan kudurori, yana mai jaddada cewa, hakkin Iran na ci gaba da kasancewa a karkashin dokokin kasa da kasa.
Qalibaf ya bayyana cewa takunkumin da aka tanadar a cikin wadannan kudurorin ba su da tasiri sosai fiye da takunkuman Amurka, kuma aiwatar da su a matakin Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar cikas mai tsanani na shari’a. Sai dai kuma ya yi gargadin a lokaci guda cewa: Idan har kowace kasa ta aiwatar da wadannan kudurori da suka saba wa doka kan Iran, to za ta fuskanci martani mai tsanani kuma kai tsaye, sannan kasashen Turai uku za su ga matakin da Iran ta dauka a fili.