Ƙungiyar gwagwarmaya Falasdinawa ta Hamas, ta ce an kashe shugabanta na Lebanon Fateh Sherif Abu el-Amin tare da iyalansa a wani hari da Isra’ila ta kai a kudancin kasar.
Bayanai sun nuna cewa wani jirgi mara matuki na Isra’ila ya kai hari a hawa na biyar na wani gida a kan hanyar da ta hada Beirut da Filin Jirin Saman kasa da kkasa na Rafik Hariri.
Daga bisani kungiyar (PFLP) ta tabbatar da cewa harin ya kashe shugabanninta uku: Mohammed Abdel Aal, wani mamba na ɓangaren siyasarta kuma shugaban sashen soja da tsaro; Imad Ouda, kwamanda soji na Lebanon, da Abdel Rahman Abdel Aal, wanda ba a bayyana matsayinsa ba.
Dakarun Isra’ila sun kaddamar da hare-hare ta sama da sanyin safiyar Litinin a yankin Kola na birnin Beirut, wanda ya kasance irinsa na farko da suka kai a cikin babban birnin na Lebanon tun da suka soma yaki da Hezbollah a watan Oktoban da ya wuce.