Shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ya tsallake yunkursin tsige shi, sakamakon ayyana dokar ta-baci da ya yi, bayan da ‘yan majalisar dokoki daga jam’iyyarsa mai mulki suka kaurace wa kada kuri’ar duk da zanga-zangar da aka yi a wajen majalisar.
A daren ranar 3 ga watan Disamba, Yoon ya baiwa al’ummar kasar da al’ummar duniya mamaki ta hanyar ayyana dokar soji lamarin da ya fusata ‘yan kasar da dama.
Jam’iyyun adawa ne suka gabatar da kudirin tsige shi, wanda ke bukatar kuri’u biyu bisa uku kafin a amince da shi.
Lamarin dai ya tilastawa ministan tsaron kasar mika takardar murabus dinsa tare da baiwa jama’ar kasar hakuri.
Shi dai Shugaba Yeol na kasar Koriya ta Kudu ya kafa dokar ta-baci lokacin wani jawabi da ya gabatar kai tsaye ta kafofin yada labarai rarar Talata, lamarin da ya fusata ‘yan kasar da dama.
Shugaban ya ce ya kafa dokar ta-bacin ne domin magance ‘yan kanzagin Koriya ta Arewa da tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar game da ‘yancin fadin albarkacin baki.