Search
Close this search box.

Shugaban Kasar Senegal Ya Bukaci Mayar Da Yahudawan Sahayoniyya Saniyar Ware

Fira ministan Senegal ya yi kira da a mayar da haramtacciyar kasar Isra’ila saniyar ware tare da yin kakkausar suka kan Netanyahu Fira Ministan Senegal

Fira ministan Senegal ya yi kira da a mayar da haramtacciyar kasar Isra’ila saniyar ware tare da yin kakkausar suka kan Netanyahu

Fira Ministan Senegal Usman Sonko ya zargi takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ci gaba da yakin Gaza don kare matsayin siyasarsa, yana mai ba da shawarar mayar da haramtacciyar kasar ta Isra’ila saniyar ware don kawo karshen dabi’ar dabbanci da wasu kasashen yammacin Turai suka amince da ita.

A jawabin da ya gabatar a zaman taron nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a Masallacin birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal: Fira ministan kasar ta Senegal Usman Sonko ya bayyana cewa: Suna ganin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ikonsa ya dogara da wannan yaki da yake yi, kuma rayuwar siyasarsa ta dogara da wannan yakin, kuma a shirye yake ya yi tafiya a kan dubban gawarwaki don ci gaba da zama a kan karagar fira minista don kada ya fuskanci shari’a a kasarsa.

Sonko ya kara da cewa: Dole ne a hada kai da duk wanda ya yi Allah wadai da wannan rashin adalci, kuma a hadu a yi aiki don cimma matsaya ta siyasa wajen mayar da haramtacciyar kasar Isra’ila saniyar ware wanda haka ne mafita ta warewar dambaruwar siyasar Falasdinu, yana mai jaddada cewa lamarin na da alaka da dakatar da wannan dabbanci wanda wasu kasashen yammacin duniya suka amince da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments