Shugaba José Raúl Mulino Quintero ya ce mashigar ruwan mallakin kasarsa Panama ce, kuma za ta cigaba da zama a hakan tare da girmama hakkin kowadanne kasashe wajen cin moriyarta.
Shugaba José Raúl Mulino Quintero ya mayar da martani ne ga shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya riya cewa mashigar za ta koma karkashin Amurka.
HAka nan kuma shugaban kasar ta Panama wanda ya yi wa al’ummar kasarsa jawabi ya kara da cewa, babu wata kasa a duniyar nan wacce take tsoma baki wajen tafiyar da harkokin mashigar ruwan, kuma sakamakon gwgawarmayar al’ummar kasar ne na shekara da shekaru ya sa aka kulla yarjejeniyar
Torrijos–Carter a 1977.
Haka nan kuma ya ce,tun daga wancan lokacin zuwa yanzu, kasar ta Panama ta ci gaba da kula da tafiyar da wannan mashigar.
A jiya Asabar ne dai shugaban kasar ta Amerika ya sanar da cewa zai kwace iko da wannan mashiga, yana mai zargin kasar ta Panama da mika wa China tafiyar da shi.
Shugaban kasar ta Panama ya yi watsi da wannan zargin yana mai cewa mashigar ruwan tana nan a karkashin ikon kasarsa, kuma babu wata kassa da take tsoma baki wajen tafiyar da ita.
Da safiyar yau Talata shugaban kasar ta Amurka ya bayarwa da umaranin a sauyawa mashigar suna daga ta Panama zuwa ta Amurka.