Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya Ya Koma Gida Bayan Batan Dabo Na Makwanni 10

Shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya mai shekaru 93 ya kokma kasarsa bayan da ya dauki makwanni 10 ba a san inda ya tafi ba.
komawar {aul Biya Gida

Shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya mai shekaru 93  ya kokma kasarsa bayan da ya dauki makwanni 10  ba a san inda ya tafi ba.

A lokacin da ya bar kasar, makusantan shugaban kasar ta Kamaru sun ce za iyi tafiya ne ta gajeren lokaci, said ai kuma dadewar da ya yi ta sa ana sa alamar tambaya akan yanayin lafiyarsa.

A cikin kasar ta Kamaru an rika yin kira da a bayyana cewa babu kowa akan kojerar shugaban kasar da hakan zai bayar da damar maye gurbinsa.

Sai dai duk da cewa a halin yanzu ya koma gida, kuma ya rattaba hannu akan dokoki masu yawa, hakan ba zai kawo karshen tattaunawar da ake yi ta makomar kujerar  shugaban kasar ba.

 Shi dai Paul Biya,ba shi da mataimaki, kuma tabarbarewar lafiyar ta na kara wa ‘yan adawa kaimi akan batun samar da sauyi a cikin harkokin siyasar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted