Shugaban Kasar Iran:Kasashen Musulmi Za Su Iya Dakatar Da Laifukan HKI

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizizhkiyan wanda yake halartar taron kungiyar D8 a kasar Masar ya bayyana cewa; Ta hanyar aiki tare, kasashen musulmi za su

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizizhkiyan wanda yake halartar taron kungiyar D8 a kasar Masar ya bayyana cewa; Ta hanyar aiki tare, kasashen musulmi za su iya  dakatar da  laifukan da HKI take tafkawa.

Shugaban kasar ta Iran ya ce ta fuskokin shari’a doka da ‘yan’adamtaka, kasashen musulmi, za su iya daukar matakan da su ka dace cikin gaggawa da za su iya kai dauki ga ‘yan’uwansu musulmi dake cikin ibtila’i.

Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; A halin yanzu an shiga watanni na 14 da yammacin Asiya,musamman a Gaza, kudancin Lebanon da kuma Syria, muke ganin hare-haren da HKI take kai wa.

Har ila yau, Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda HKI take kisan kiyashi na mata da kananan yara da ta’addancin akan fararen hula,ba don komai ba sai saboda cimma wasu manufofi da suke haramtattu. Haka nan kuma ya ce nauyi ne akan musulmi da su kawo karshen abinda yake faruwa a Gaza.

A wani sashe na jawabin shugaban kasar ta Iran ya tabo maganar kirkirarriyar Basira ( AI) wacce yake da akwai bukatar a hada karfi da karfe wuri daya domin sa ido akan tafiyar da ita,domin kaucewa illolinta. Haka nan kuma ya bukaci ganin an yi amfani da fasahar ta zamani domin bunkasa tattalin arzikin kasashen da suke mambobi a wanann kungiyar ta D8.

Dangane da samarwa samari masu fasahar kirkira aikin yi shugaban kasar ta Iran ta bukacin ganin kungiyar ta D8 ta yi wani yunkuri na bai daya da kuma kafa Banki na haidin  gwiwa domin cimma wannan manufa.

A yau Alhamis ne dai aka bude taron kungiyar D8 wacce ta hada kasashen Masar, Iran, Turkiya, Nigeria  Bangaladesh, Malyasia, Indonesia  da Pakistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments