Shugaban kasar Iran ya taya Fafaroma Francis shugaban darikar Catholika ta mabiyar addinin Kiristan murnar zagayowar Kirsimeti
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a cikin wata wasika da ya aikewa Paparoma Francis ya taya shugaban darikar Catholika ta Mabiya addinin Kiristan Paparoma na Vatican murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya kara da cewa: Bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa {Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi} wata dama ce ta tunawa da koyarwar Ubangijin na wannan annabi mai girma wanda yake kira ga kowa da kowa zuwa ga wanzar da adalci da aminci da soyayya.
A yayin bukukuwan Kirsimeti da kuma zagayowar ranar haihuwar Almasihu dan Maryama (amincin Allah ya tabbata a gare shi), shugaban kasar Masoud Pezeshkian, ya aike da sakon taya murna ga Fafaroma Francis, Paparoma na Vatican, inda ya jaddada cewa girmama zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana wakiltar ginshiƙi na ɗabi’a don tunawa da dokokin Allah da kuma koyarwa masu kima na dukkan annabawa don tabbatar da adalci, aminci da ’yanci. Pezashkian ya kara da cewa: Al’umma a wannan zamani da muke ciki na bukatar sabon hangen nesa don tunkarar al’amuran al’ummomin bil’adama, don haka tunani da yin la’akari da madaukakan halayen annabawan Ubangiji na iya zama wata hanya ta dan Adam na wannan zamani don cimma kamalar dan Adamtaka.