Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Gudanar Da Hidima Ga Al’umma Daga Kowane Dan Kasa

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Gudanar da hidima wa mutane aikin kowa ne Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa yi wa al’umma

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Gudanar da hidima wa mutane aikin kowa ne

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa yi wa al’umma hidima aiki ne na kowa da kowa, yana mai bayanin cewa hadin kai da fahimtar juna kan kasa suna samun nasarar gudanar da mulki da tsayin daka wajen tunkarar makiya.

A yayin jawabin da ya gabatar a wajen bikin sabunta mubaya’ar Imam Khumaini (r.a) a hubbarensa mai tsarki da ke birnin Tehran, shugaban kasar Masar Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: “Aikin hadin kan jama’ar kasa ne yi wa al’umma hidima da nuna musu kauna, idan har za a iya tabbatar da adalci a cikin halayen al’umma, za a yi nasara wajen hidimtawa al’umma, kuma dukkan jami’ai za su zama bayin mutane.”

Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa yi wa jama’a hidima da sauraron muryoyinsu wani aiki ne na kowa da kowa. Ya yi imanin cewa, abin da zai iya cimma nasara shi ne hadin kai da fahimtar juna kan kasa, kuma duk wani abu da zai cutar da wannan hadin kan ba za a amince da shi ba. Ya bayyana cewa, idan aka samu hadin kai, makiya Amurka da gwamnatin sahayoniyya ba za su kuskura su kai hari ko wuce gona da iri kan kasar Iran ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted