Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan, wanda yake kan hanyarsa ta zuwa birnin NewYork na kasar Amurka don halattar babban taron shuwagabannin kasashen duniya na shekara shekara karo na 81, ya yada zango a birnin Aljeis babban birnin kasar Aljeriya a yau Talata.
Kamfanin dillancin labaran Iran na kasar Iran ya bayyana cewa ministan harkokin cikin gida na Aljeriya ne ya tarbi shugaban a tashar jiragen sama na Aljeriya na dan lokacinda zai huta a tashar kafin ya wuce.
Kafin ya bar Tehran shugaban ya bayyana cewa a jawabin da zai gabatar da kuma gane ganen da shi da tawagarsa zata yi da sauran shuwagabannin duniya, zasu isar da matsayin Iran da kuma damuwar mutanen kasar kan yakin da Amurka ta dorawa kasar da kuma takura masu da tayi ga kasashen duniya.
Ya ce, tare da goyon bayan mutanen kasar zata ci gaba da jajircewa kan matsayinsu, da kuma neman hakkinsu ko menene hakan zai kaishu gareshi.