An yi ganawa a tsakanin shgabannin kasashen Amurka Donald Trump da Gustavo Perto na Columbia a fadar “White House” da hakan yake nuni da sauyi a alakar kasashen biyu.
Donald Trump ya fada wa ‘yan jarida cewa; Ganawar ta yi armashi sosai” sannan ya kara da cewa, a baya babu gaskata juna a tsakaninsa da shugaban na Columbia amma rashin haduwarmu ne ya jawo hakan.”
Watanni kadan a baya shugaban kasar ta Amerika ya rika sukar takwaransa na Columbia tare da tuhumarsa da dillancin muggan kwayoyi. Haka nan kuma ya yi barazanar amfanida karfin soja domin kai wa kasar ta Columbia hari.
Sai dai a wannan haduwar shugaba Donald Trump ya bayyana Petro da cewa; mutum ne na musamman”
A nashi gefen, shugaban kasar ta Columbia Perto Gustav ya fadawa taron manema labaru cewa; Ganawar tasu ta yi armashi, kuma muhimmin jigon da su ka mayar da hankali akansa a tattaunawar shi ne “Yanci. Haka nan kuma ya ce wasu daga cikin abubuwan da su ka tattauna da akwai aiki tare domin fada da muggan kwayoyi da kuma tattalin arziki.