Shugaban Iran Yace Iran Ba za ta Mika Wuya Ga Matsin Lamba Ba

shugaban kasar iran ya nuna cewa iran ba za ta amince da mika wuya ga matsin lamba ko tislatawa ba

Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayya cewa Tehran ba zata taba mika wuya ga matsin lamba ba,ko kuma ta bari wani karfi daga waje ya tilasta mata amincewa da bukatunsa ba, ya jaddada cewa iran za ta kare hakkokinta karkashin dokokin kasa da kasa

Shugaban na iran ya fadi haka ne a jiya talata a wata ganawa da yayi a kebe da sabbin jakadun kasashen waje da suka kama aiki a nan birnin Tehran na kasahen Portugal, Swizerland, turkiya, da kuma kasar najeriya  da suka mika takardun kama aiki a nan Tehran ga sugaban kasar ta iran

Haka zalika shugaban kasar iran yayi tir da ta’aadancin kasa da kuma kai hari kan masana da daliban makaranta da shuwagabannin siyasa a yankin da Amurka da hki suka yi , wanda suka aikata wannan aikin suna ikirarin fada da ta’addanci lokacin da suke ta’assar, wannan shi ne gaskiya mai daci da duniya take fuskanta

Da yake ganawa da sabon jakadan najeriya a birnin Tehran Alh Hamza mohammad Salao pezeshkiyan ya nuna fatansa na kara samun dangantaka mai karfi tsakanin Tehran da birnin tarayya Abuja, yace iran a shirye take ta yi amfani da damar da take da shi wajen bunkasa alaka mai karfin da najeriya, kuma tana maraba da  duk wani mataki da zai karfafa hakan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted