Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu ya gana da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a nan Tehran a jiya litinin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a ganawar, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan yace kyautata dangantaka tsakanin Iran da Rasha na daga cikin al-amura masu muhimmanci wadanda JMI ta sa a gaba. Shugaban ya bukaci a gaggauta aiwatar da yarjeniyoyin da ke da su tsakanin kasashen biyu.
Pezeskiya ya kara da cewa, yayi imani kan cewa zamanin kasa guda, kamar Amurka ta yi ta jujjuya duniya kamar yadda taga dama ya wuce. Don haka Iran tana da ra’ayin samar da kasashe masu karfi a duniya wadanda zasu yi aiki don ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya gaba daya. Ya kara da cewa kasashen Rasha da Iran suna aiki tare don tabbatar da cewa an sami wasu kasashen masu cikekken yenci daga Amurka, kuma zasu tsayawa kansu don cimma manufofinsu.
Yace wannna ne zai iya samar da zaman lafiyaa mai dorewa a duniya. A wani bangare na jawabinsa shugaba Pezeshkiyan ya tabo batun abinda yake faruwa a kasar Falasdinu da aka mamaye, da kuma kissan shugaban kungiyar Hams a birnin Tehran wanda HKI ta yi. Yace, Iran tayi allawadai da kasashen Amurka da kuma na yamma kan irin goyon bayan da suke bawa HKI bisa ta’asan da take aikatawa a Gaza.
A nashi bangaren babban sakatarin majalisar koli ta tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu, da farko ya taya Pezeshkiyan murnar zaben sa a matsayin shugaban kasar Iran, ya kuma kara da cewa kasar Rasha tana fatan tare da kasar Iran zasu samar da duniya inda ba kasa daya ta ke yin abinda taga dama ma. Sannan ya bayyana bukatar a kara fadada dangantaka da kasar Iran a cikin al-amura daban daban.