Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Masoud pezeshkiyan ya jaddada matsayin iran wajen riko da diplomasiya, amma tayi watsi da duk wani babakeren Amurka, kuma ya bayyanawa shugaban rasha Vladmir putin cewa kasar iran ba za ta bar teburin tattaunawa ba ko da Washington ta ci gaba da kai hare-hare
A lokacin ganawarsa da shugaban kasar rasha agefen taron kolin kungiyar kasashe masu cin gashin kansu, da kuma taron kolin kare muhalli na tekun caspia a birnin turkmenbashi na kasar turkmenistan yace mun ci gaba da tattaunawa duk da cewa duk lokacin da muka fara tattaunawa da amurka sai ta kaddamar da sabbin hare hare, amma duk da haka ba zamu bar teburin tataunawa ba,
pezeshkiyan ya godewa kasar rasha game da matakin da ta dauka a matsayin kasa da kasa da kuma majalisar dinkin duniya har kuma da rawar da yake takawa wajen dakile yunkurin daukar matakai na kai tsaye ba tare da tuntubar wasu ba.
Daga karshe ya nuna cewa babban burinmu shi ne kawo karshen duk wani rikici da kuma ganin an girmama hakkin iraniyawa karkashin dokokin kasa da kasa, sai dai idan Amurka ta dage wajen daukar matakai ita kadai hakan ba zai yi wu ba