Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Al’ummar Iran ba za su mika wuya ga matsin lamba ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Amurkawa suna neman Iran ta mika wuya ga munanan manufofinta, yana mai jaddada cewa, mutanen Iran ba za su mika wuya ga duk wani matsin lamba daga masu girman kai ba.
A cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X-platform, Shugaba Pezeshkian ya rubuta cewa: “Cika alkawari shine kawai tushe mai ma’ana da kuma hujja ga kowace irin tattaunawa.” Ya kara da cewa, baya ga rashin amincewar da Iran ta yi wa ayyukan da gwamnatin Amurka ta yi a baya, rashin ingantaccen tsari da sabani da jami’an Amurka suka yi a ‘yan kwanakin nan yana dauke da sako daya mai zafi: suna son Iran ta mika wuya ga munanan manufofinsu ta girman kai, yayin da al’ummar Iran ba za su taba mika wuya ga masu girman kai ba.
Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ne a yankin Gabas ta Tsakiya kuma tana tabbatar da haƙƙin al’ummarta a cikin tsarin dokokin ƙasa da ƙasa.