Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya ya ce: Ana ci gaba da tuntubar juna game da Iran, kuma cimma yarjejeniya na buƙatar cikakken tsari
Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da cewa: Ana ci gaba da tuntubar juna da tattaunawa game da Shirin makamashin nukiliyar Iran.
Grossi ya shaida wa manema labarai cewa: Karo na karshe da tawagar masu bincike ta IAEA ta ziyarci cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran da aka kai wa hari shi ne ‘yan kwanaki kafin hare-haren a watan Yunin bara.
Ya jaddada cewa: Cimma yarjejeniya da Iran na bukatar cikakken tsari wanda ya shafi dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa ba tare da irin wannan tsari ba, ba za a iya cimma yarjejeniyar ba.
Tun da farko a ranar Laraba, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar da cewa: Shugaban Hukumar na IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: A shirye yake ya bayar da goyon baya wajen shirya tsarin tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da Amurka.