Rafael Grossi babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA a wata hira da yayi da gidan talbijin din Russia 24 ya bayyana cewa shirin nukiliya iran na zaman lafiya ne baki daya.
Wannan maganar ta yi karo da kalaman prime minister isra’ila Benjamin Natanyaho inda ya nuna cewa shirin nukiliyar Iran babban barazana ne, don haka kalaman na shugaban IAEA sun tabbatar da ikirarin da iran ta dade tana yi na cewa shirin na zaman lafiya ne.
Grossi ya fadi cewa ya amince hare-haren soji sa israila ta kai sun auna cibiyoyin nukiliyarta ta Fordo Natanza da kuma Isfahan inda ake ci gaba da inganta sinadarin yunariyum.
Ya tabbatar da cewa iran ta tace yuraniyom kashi 60% , amma kasar ba ta kai iyakar inda za ta kera makamin nukiliya ba,