Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta.
Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar.
Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES.
Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel.
Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin arziki da tsaro.
Kafin Nijar, John Dramani Mahama ya je Mali inda Janar Assimi Goïta ya tarbe shi. A cewar fadar shugaban kasar Ghana, ganawar da aka yi tsakanin mutanen biyu ta ba da damar fara tattaunawa kan karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro.
Shugaban na Ghana ya kuma yi amfani da wannan dama wajen bayyana mahimmancin kasuwanci ta hanyar tashoshin jiragen ruwa na Ghana da ke Tekun Atlantika ga Mali.