Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan kasarsa, yana mai jaddada cewa Havana a shirye take ta kare kanta “har zuwa digon jini na karshe.”
Shugaba Diaz-Canel ya yi wannan tsokaci ne bayan da Trump ya yi ikirarin cewa babu wani karin mai ko kudi na Venezuela da zai je Cuba bayan kame Shugaba Nicolas Maduro da sojojin Amurka na musamman suka yi.
Shugaban Cuba ya mayar da martani ta hanyar jaddada cewa Cuba kasa ce mai ‘yanci, da cin gashin kanta, kuma babu wanda ke da ikon tsara abin da ya kamata ta yi.
Tunda farko Ministan Harkokin Wajen Cuba Bruno Rodriguez ya ce kasarsu tana da ‘yancin shigo da mai daga duk wani mai samar da mai da ke son fitar da shi.
Ya kuma musanta cewa Cuba ta sami diyya ta kuɗi ko wasu “kayan aiki” a madadin ayyukan tsaro.
A ranar 3 ga Janairu, sojojin Amurka sun kame Maduro da matarsa daga Caracas suka nufi New York dasu bayan kai mummunan hari a kasar.
Harin soja a kan Venezuela ya biyo bayan watanni na matsin lamba a kan kasar a bisa fakewa da yaki da miyagun kwayoyi zuwa Amurka.
Caracas ta musanta duk wata alaka da fataucin miyagun kwayoyi kuma ta dage cewa Washington na da niyyar hambarar da shugaban Venezuela a yunkurin kwace iko da babban rumbunan mai na ƙasar.