Shugaba Trump Yace Zai Gana Da Shugaban Kasar Iran A New York

A wani labarin kuma shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai gana da shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan a birnin NewsYork saboda kawo

A wani labarin kuma shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai gana da shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan a birnin NewsYork saboda kawo karshen tsadar man fetur wanda rufewar mashigar ruwa ta Hurmuz ta jawao.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya ce bayyana cewa shugaban bai bayyana yanda ganawar zata kasance ba.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka ya sha nanata maganar cewa Amurka a shirye take ta tattauna da Iran kai tsaye don kawo karshen yakin, amma tana son daga karshe Iran ta mika kai ga bukatunta.

A wani bangaren shugaban ya bayyana cewa yana tunani da kuma bincike dangane sharuddan da JMI ta sanya don bude mashigar ruwa ta Hurmuz. Banda haka shugaban ya sha nanatakan cewa, zai kawo karshen yaki da Iran nan kusa, amma ba abinda yake faruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted