Shugaban kasar Iran Dr. Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana cewa; Sai idan kasashen wannan yankin sun yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu ne za a iya samun tsaro mai dorewa a yankin tekun Pasha da kuma hanyoyin ruwa.”
Shugaban kasar ta Iran wanda a aike da sako dangane da ranar sufurin ruwa ta duniya ya bayyana cewa, ruwa da teku da Iran take da su, wata baiwa ce daga Allah kuma wani sashe ne mai muhimmanci na tarihin wannan kasa, wanda zai ci gaba da zama mai muhimmanci har zuwa gaba.
Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce; Yi wa teku kyakkyawan sani da kuma kera kayan aiki na zamani domin amfani da su a cikin teku, da bunkasa hanyoyin kariya daga hatsurra, suna daga cikin zuba jari na hakika da kasa za ta yi domin bunkasa rayuwa ta manyan gobe masu zuwa.
Haka nan kuma ya ce; Wajibin da yake a wuyan gwamnati shi ne saukake hanyoyin aiki da kawar da duk wani cikas da kuma aiki a tsakanin bangarori mabanbanta na gwamnati da zai samar da zuba hannun jari saboda share fagen shigar mutane da yawa cikin wannan fage da kuma samar da kamfanoni masu zaman kansu.
Da kuma yake Magana akan mashigar Ruwan “Hurmuz” da samar da tsaro a fagen kasuwanci na wannan yankin da kuma duniya, shugaban kasar ta Iran ya yi kira da a samar da wata mahanga kaan kare manufofin kasashen wannan yankin.