Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Juyayin Shahadar Haniya Bayan Shekara Guda Da Shahada

Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa

Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da  Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar.

Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu murnin zama shugaban kasa.

Shugaban yace da yardarm All.. Iran ba zata taba manta da haniyya ba. Da kuma al-amarin kasar Falasdinu. Zamu yi maganin HKI da Amurka saboda ta’asan da suke aikatawa a kasashen yankin, kama daga Gaza zuwa sauran yankunan Falasdinawam yankin yamma da kogin Jordan, da kuma ayyukan ta’adancin da take aikatawa a yankin, wanda ya hada da Lebanon da kuma Siriya.

Ya ce: kasar Iran tana kan alkawalinta kan kare kasar da kuma al-amarin Falasdinawa.  A jiya jumma’a ma, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan zagayowar shekara guda da shahadar shugaban kungiyar Hamas marigayi Isma’ila Haniyya. Wanda makiya JMI tare da taimakon kasashen Amurka da HKI suka kashe shi a masaukinsa a nan birnin Tehran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted