Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian yayin da yake jinjinawa bayanan goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a ranar Lahadin da ta gabata ya rubuta cewa: “Ina mika godiya ta musamman ga Jagora bisa kyakkyawan ra’ayi da goyon bayan da yake bayarwa, mu saurari shawararsa ta hadin kai da hadin kan kasa daga gare shi.”
Shugaba Masoud Pezeshkian yayi wannan jinjina ne biyo bayan jawabin goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya baiwa yunkurin hadin kan kasa da hadin kan al’ummar kasa.
Pezeshkian ya rubuta a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadin da ta gabata cewa: “Bisa da kokarin ganin an hidimtawa al’ummar kasa, jagora bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da shawawarwari da kuma shiryarwa ga dukkanin bangarori, kama daga shugaban kasa har zuwa sauran jami’ai a dukkanin bangarori, da sauran fagage na al’ummar kasar Iran.