Shugaba Pezeshkian Ya Isa Masar Domin Halartar Taron D-8

Yau Alhamis ake fara taron koli na kasashen gungun D-8 a birnin Alkahira na kasar Masar. Kungiyar ta tsakanin kasashen musulmin 8 na mayar da

Kungiyar D-8 A Masar

Yau Alhamis ake fara taron koli na kasashen gungun D-8 a birnin Alkahira na kasar Masar.

Kungiyar ta tsakanin kasashen musulmin 8 na mayar da hankali kan inganta hadin gwiwar tattalin arziki, da samar da ci gaba, a tsakanin mambobinta.

Shugaba Massoud Pezeshkian na Iran, na daga cikin mahalarta taron.

Ziyarar tasa ita ce irinta ta farko ta wani shugaban kasar Iran a Masar cikin shekaru 11, bayan wacce tsohon shugaba Mahmoud Ahmedi Nedjad ya kai a 2013 inda ya halarci taron OIC.

Kafin tafiyarsa shugaba Pezeshkian ya bayyana irin gagarumar rawar da Masar take takawa a duniyar Musulunci, yana mai bayyana ta a matsayin “kasa mai dogon tarihi da wayewa mai girma da ke taka rawa a duniyar Musulunci.”

Shugaban ya kara jaddada muhimmancin kulla alaka mai karfi a tsakanin kasashen musulmi, inda ya kara da cewa: “Idan dangantakarmu ta kara kusanci, da zurfafa, to za mu iya dakile makircin makiya a kanmu da sauran kasashen musulmi.”

Ya kuma kara da cewa, tattaunawar da za a yi a yayin taron, za ta kunshi muhimman batutuwan da suka shafi Gaza, Falasdinu, da Lebanon.

Tattaunawar dai na da nufin lalubo hanyoyin da kasashen musulmi za su iya daukar matsaya daya na kare hakkin wadanda ake zalunta a Gaza, Lebanon da Syria.

Kungiyar D-8 wacce aka kafa a 1997 ta hada Kasashen Turkiyya, Iran, Pakistan, Bangladesh, Indonesia, Malaysia, Masar, da Najeriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments