Shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya isa Minsk, babban birnin kasar Belarus, bayan gayyatar da takwaransa na Belarus Alexander Lukashenko ya yi masa.
Shugaban na Iran ya sauka a kasar Belarus a yammacin jiya Talata domin ziyarar aiki da nufin karfafa alakar kasashen biyu.
A yayin ziyarar tasa, shugaba Pezeshkian zai gana da shugaba Lukashenko da shugaban majalisar wakilai ta Jamhuriyar Belarus Vladimir Andreichenko.
Bugu da kari, Pezeshkian zai gana da al’ummar Iran da ke zaune a Belarus domin tattauna batutuwan da suka shafi ayyukansu da kuma da kuma bangarorin da gwamnatinsa za ta iya taimaka musu da karfafa musu gwiwa.
Ana sa ran a wannan ziyarar za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama tsakanin Iran da Belarus, da kuma kara habaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Iran da Belarus dai suna da tsohuwar alaka ta diflomasiyya, da ayyukan hadin gwaiwa a bangarori da dama na tattalin arziki, taro kasuwanci da kuma ilimi da al’adu.