Iran Da Belarus Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyi A Tsakaninsu

Kasashen Iran da Belarus sun rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa da takardun hadin gwiwa 12 Manyan jami’ai daga Iran da Belarus sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa 12 da kuma sanarwar hadin gwiwa yayin ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a birnin Minsk. Manyan jami’ai daga kasashen Iran da Belarus a gaban […]

Ministan Tsaron Kasar Iran Ya Ce: Sun Kara Karfafa Ci Gaba Makamansu Masu Linzami

Ministan Tsaron Iran ya bayyana cewa: Suna da karfin makamai masu linzami fiye da wadanda suka yi amfani da su Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya yi barazanar mayar da martani mai karfi da zafi ga Amurka da Isra’ila idan suka sake kai hare-hare kan kasarsa. Yayin ganawarsa da jami’an soji a Tehran, […]

Gebran Bassil Ya Ce: Masu Neman Kwance Makaman Hizbullah Suna Neman Yaki Ne A Lebanon

Shugaban jam’iyyar al-tayyarul-Watani-Hurr ta Lebanon ya ce: Masu alfahari da murnar ganin an kwance makaman kungiyar Hizbullahi suna son bullar yakin cikin gida ne a Lebanon Shugaban jam’iyyar al-tayyarul-Watani-Hurr ta Lebanon Gebran Bassil ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ta janyo zubar da jinin shahidai a cikin sojojin Lebanon da kuma duk mutumin da ya sadaukar da […]

Qatar:  Hamas Ta Amince Da Sabuwar Yarjeniya Da HKI

Gwamnatin kasar Qatar a birnin Dubai ta bada sanarwan cewa kungiyar Hamas ta amince da wata yarjeniya wacce HKI ta amince a baya, don haka akwai fatan HKI zata sake amincewa da ita sannan a tsagaita budewa juna wuta nan gaba kadan. Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto kakakin […]

Gagarumar Zanga-Zanga A São Paulo Kan Gaza Ta Hana Jakadan Isra’ila Magan

Gagarumar zanga-zanga wanda daruruwan mutane suka gudanat a birnin São Paulo na kasar Brazil wannan ya hana jawabin jakadan HKI a karamin ofishinn jakadancin Amurka dake birnin., . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa masu zanga zanga sun hana jakadan shiga yalin da ofishin jakadancin Amurka ke kansa don gudanar da […]

An Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Shekara Ta 2026 A Kasar Uganda

An fara yakin neman zabe a kasar Uganda don zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a shekara ta 2026 mai zuwa., inda jam’iyya mai mulki da kuma jamiyyun adawa duk sun fara yakin neman zabe. A ranar 19 ga watan Augustan da muke ciki ne, jam’iyyar shugaban kasa ta ‘National Resistance Movement (NRM), ta gabatar […]

Gaza: Masu Neman Abinci 31 Ne Suka Yi Shahada

A rana ta 684 da fara yaki a gaza masu neman agajin abinci kimani 31 ne suka yi shahada a lokacin bada wannan labarin daga cikinsu akwai mutane 8 wadanda yahudawan suka kashe a lokacinda suke jiran karban abinci a yankin Netzarin na tsakiyar gaza a tarkon kissan da HKI da Amurka suka A labaran […]

Shugaba Pezeshkian na Iran ya isa kasar Belarus

Shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya isa Minsk, babban birnin kasar Belarus, bayan gayyatar da takwaransa na Belarus Alexander Lukashenko ya yi masa. Shugaban na Iran ya sauka a kasar Belarus a yammacin jiya Talata domin ziyarar aiki da nufin karfafa alakar kasashen biyu. A yayin ziyarar tasa, shugaba Pezeshkian zai gana da shugaba Lukashenko da […]

Faransa ta mayar wa Netanyahu da martani kan zargin Macron da kyamr baki

Ministan Faransa a harkokin Turai, Benjamin Haddad, ya bayyana cewa babu wasu darussan da Faransa za ta dauka daga Isra’ila kan yaki da kyamar baki, yana mai da martani kan zargin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan Shugaba Emmanuel Macron. Da yake magana a gidan talabijin na BFMTV na Faransa, Haddad ya ce, […]

Iran, China da Rasha suna kan bakansu na kawo karshen kudiri mai lamba 2231 akan lokaci

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya gana da jami’an diflomasiyya na kasashen Sin da Rasha, game da yadda za a iya aiwatar da kudurorin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar mai kula da harkokin shari’a da na kasa da […]