Shekih Na’im Kassim: Mun Sami Nasarar Da Ta Fi Ta 2006

A jawabinsa na farko tun  bayan fara aiki da tsagaita wutar yaki,babban magatakardar kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa; Farin cikin da mutane su ka nuna

A jawabinsa na farko tun  bayan fara aiki da tsagaita wutar yaki,babban magatakardar kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa; Farin cikin da mutane su ka nuna a lokacin da suke komawa gidajensu jim kadan bayan fara aiki da tsagaita wutar yaki, shi ne dalilin da ya sa shi yin jinkirin yin jawabi a waccan rana.

Sheikh Na’im Kassim ya yi godiya ga Allah wanda shi ne ya bayar da wannan nasara, sannan kuma ya yi jinjina ga shahidai jagorori musamman Sayyid Hassan Nasrallah.

Har ila yau Sheikh Na’im Kassim ya kuma ambaci  jagororin Hibzullah da su ka yi shahada da su ka hada Sheikh  Hashim Safiyyuddin, Mustafa Badruddin, Nabil Qawuq da wasu da dama.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kaddamar da nasarar da su ka samu ga dukkanin ‘yan’tattun duniya da dukkanin wadanda su ka taka rawa wajen samar da shi, da jini ko da alkami.

Har ila yau ya kuma yi godiya ga jamhuriyar msuulunci da jagororinta da al’ummarta, musamman jagoran juyin juya hali  Imam Sayyid Ali Khamnei.

Dangane da mataki na gaba da kungiyar ta Hizbullah za ta dauka, Sheikh Na’im Kassim ya ce, za su mayar da hankali wajen sake gina rusau din da Isra’ila ta yi, haka nan kuma tabbatar da cewa an zabi shugaban kasa.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma tabbatar da cewa, gwgawarmaya za ta cigaba.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments