Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa gwagarmaya ba za ta bari a kwance damarar ta ba, kuma za ta shiga fada irin na Karbala idan hakan ya kama, ya kara da cewa: “Za mu fuskanci duk wani aiki da zai yi wa Isra’ila hidima, ko da kuwa an mayar da shi tamkar wani aiki na kasa.”
A jawabin da ya gabatar a yayin zagayowar cikar shekara guda da shahadar Sayyed Hassan Nasrallah da Hashem Safieddine, Sheikh Qassem ya mayar da martani ga kalaman manzon Amurka Tom Barrack, wanda ya ce Washington na son kwance damarar kungiyar Hizbullah, kuma ba za ta ba sojojin makamai domin tunkarar Isra’ila ba. Ya kara da cewa ” kwance damarar makamai na nufin kwance damarar dakarun gwagwarmaya bukata ce ta Isra’ila domin cimma manufofinta.
Sheikh Qassem ya yi kira ga gwamnatin Lebanon da ta cika aikinta na sake gina wuraren ‘ya kasar da Isra’ila ta rusa tare da ware kasafin kudi domin hakan, koda kuwa kadan ne. Ya nanata cewa Fifita maslahar kasa dole ne ya kasance kan gaba a cikin ajandar, kuma cimma hakan na bukatar hana Isra’ila ci gaba da zama a Lebanon.
Ya kara da cewa kiyaye hadin kai na cikin gida da kuma yin aiki don farfado da kasar Labanon ya zama wajibi, kuma gwagwarmayar al’ummar kasar ita ce tushen karfinta.
Ya kuma yi kira da a aiwatar da yerjejeniyar Taif, wadda ta tanadi cimma nasarar ‘yantar da dukkanin yankunan kasar Lebanon da Isra’ila ta mamaye ta hanyar gwagwarmaya.
Ya ci gaba da cewa, “Muna goyon bayan gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a kan lokaci,” yana mai cewa “gwamnati ta yi wani babban kure a lokacin da ta yanke shawara kan batutuwa da suka shafi makaman Hizbulah.”
Ya kara da cewa, suna son sojojin kasar Lebanon su yaki mutanensu, kuma muna goyon bayan sojoji wajen tunkarar makiya na hakika, kuma a kodayaushe muna tare da su.