Sheikh Qaseem: Kwance Damarar Hizbullah, Shiri Ne Na Amurka Da HKI

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’eem Qaseem ya bayyana cewa shirin kwance damarar mayakan kungiyarsa shiri ne na HKI da Amurka, ko da

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’eem Qaseem ya bayyana cewa shirin kwance damarar mayakan kungiyarsa shiri ne na HKI da Amurka, ko da sun kira shi takaita makamai hannun gwamnati, kuma Lebanon ba zata taba fita cikin matsalolin da take ciki ba matukar HKI bata aiwatar da shirin tsagaita wuta da aka cimma da ita a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 ba.

Tashar talabijan da Al-Manar ta kungiyar wacce ta watsa jawabin Hujjatul Islam Sheikh Na’eem Qaseem kai tsaye a dazu-dazun nan ta nakalto shi yana cewa, kasar Lebanon a halin yanzu tana cikin matsaloli wadanda Amurka da HKI suka samar da su, ya ce Amurka a halin yanzu tana yada fasadi a kasar Lebanon kuma tana iko da wasu sassa da dama na gwamnatin kasar Lebanon. Ta kakabawa sassan gwamnatin kasar da dama takunkuman tattalin arziki a kokarinta na cimma manufofinta a kasar.  Shugaban ya kara da cewa bai kamata gwamnatin kasar Lebanon ta zama dan amshin shatan HKI da Amurka, don yin haka kha’inci ne ga mutanen kasar da kuma diyaucinsu. Ya ce mai yuwa HKI ta sake farwa kasar Lebanon da yaki, amma ta kwana da sanin cewa ba za ta cimma manufofinta a kasar Lebanon ba.  Y ace ‘Ku haw mafi munin dawakanku, ta aikata mafi munin abinda zaku aikata tare da taimakon mafi munin mutane, kungiyar Hizbullah ba zata mika kaiba, ba zata jada baya ba, zata ci gaba da kare kasar Lebanon har zuwa nasara da yardar Allah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted