Sheikh Qassim: Babu Batun Tattaunawa Kan Makaman Kungiyarsa

Babban Sakataren Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa; Ba ​​za su tattaunawa game da makamansu da ‘yan gwagwarmaya ke amfani da su ba

Babban Sakataren Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa; Ba ​​za su tattaunawa game da makamansu da ‘yan gwagwarmaya ke amfani da su ba matuƙar ‘yan mamaya suna ci gaba da cin zarafi

Babban Sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim ya tabbatar da cewa: Kungiyar gwagwarmaya da ake nunawa a Lebanon za ta ci gaba da fuskantar ‘yan mamayar Isra’ila, yana mai jaddada kin amincewarsa da tattauna batun makaman kungiyar muddin ‘yan mamaya suna ci gaba da wanzuwa kuma suna ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummu.

Sheikh Na’im Qassim ya bukaci janyewar sojojin mamayar Isra’ila bisa ga yarjejeniyar ranar 27 ga watan Nuwamban shekara ta 2014 da kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 ya jaddada da kuma tura sojojin Lebanon zuwa kudancin Kogin Litani.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, a cikin wata sanarwa da ya yi magana kan ci gaban siyasa a Lebanon da yankin, Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa: Yarjejeniyar ba ta da inganci saboda ta karya kundin tsarin mulki, Yarjejeniyar Taif, dokoki, rantsuwar shugaban kasa da kuma sanarwar manufofin gwamnati. Ya zargi yarjejeniyar da yin watsi da wasu muhimman abubuwa na karfin Lebanon da kuma dogaro da tayar da rikici tsakanin mabiya addinai gami da kawo cikas ga kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted