Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya yi Allah wadai da kalaman da kiraye kirayen da ake na “kwance damarar” kungiyar Hizbullah, yana mai kiransa da cewa wani yunkuri ne na raunata kasar Lebanon da kuma ci gaba da fadada manufofin Tel Aviv.
Sheikh Naim Qassem ya bayyya hakan ne a wani jawani da ya gabatar da kai tsaye ta talabijin jiya Juma’a.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a karshen shekarar da ta gabata da nufin kawo karshen kazamin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 4,000 a kasar Labanon.
Sheikh Qassem ya jaddada cewa ci gaba da kokarin da gwamnatin Isra’ila ke yi na kawo cikas ga diyaucin kasar Labanon da tsayin daka zai fuskanci martani marar iyaka.
Ya kuma jaddada cewa, karfi da hadin kan kungiyar Hizbullah da sojojin kasa da al’ummar kasar Labanon ya tabbatar da cewa gwamnatin ba za ta cimma manufofinta ba.
Sheikh Qassem ya kuma gargadi gwamnatin Isra’ila, inda ya bayyana cewa kungiyar gwagwarmayar Lebanon na da zabi da dama a gabanta dangane da keta hurumin da Tel Aviv ta yi na tsagaita bude wuta da kungiyar.