Abbas Arakci: Tattaunawa Da Amurka Ta Hanyar Shiga Tsakanin Oman Ta Shiga Sabon Zango

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Irna” cewa; An sami cimma matsaya a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka akan cewa a ranar Laraba mai zuwa za a dora daga inda akan tsaya a tattaunawar Nukiliya,” Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kara […]
Sojan HKI Ya Halaka A Gaza

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari. Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a […]
News Fox: Sau 6 Yemen Ta Kakkabo Jiragen Amurka Samfurin Mq 9 A Karkashin Gwamnatin Trump

Tashar talbijin din “News Fox” ta kasar Amurka mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ta watsa wani rahoto da yake cewa; Daga lokacin da Donald Trump ya zama shugaban kasa, sau 6 sojojin Yemen su ka kakkabo jiragen sama maras matuki samfurin Mq9. Rahoton na tashar talabijin din Fox ya kuma yi ishara da yadda sojojin […]
Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Almujtaba (a)110

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko […]
An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar

An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake […]
Amurka Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare Kan Garuruwan Sana’a, Sa’adah Da Al-Jawf Na Kasar Yemen

Kasar Yemen ta sanar da cewa: Amurka ta kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan garuruwan Sana’a, Sa’dah, da Al-Jawf Mahukuntan Yemen sun sanar da cewa: Amurka ta ci gaba da kai hare-hare kan kasar Yemen, inda ta kaddamar da wasu jerin hare-hare kan garuruwan Sana’a, Sa’dah da Al-Jawf. Wakilin Al-Alam ya ruwaito […]
Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da […]
Mayakan Kungiyar Ta’addanci Ta ISIS Sun Sake Kunno Kai A Garuruwan Deir ez-Zor Da Hasaka Na Siriya

Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces […]
Sojojin Sudan Sun Kashe ‘Yan Tawayen Kasar Ciki Har Da Manyan Kwamandojinsu A Birnin El Fasher

Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka […]
Iran da Amurka na shirin tattaunawa ta biyu a birnin Rome

Yau Asabar Washington da Tehran, ke tattauanwa a birnin Rome na kasar Italiya, wace ita ce ta biyu a shiga tsakanin kasar Oman kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Tattaunwar wacce ba ta gaba-da-gaba ba an gudanar da irin ta a ranar Asabar data gabata a birnin Muscat na kasar Oman, inda bangarorin biyu […]
Iran ta yi tir da kakkausar murya da harin Amurka kan tashar mai ta Yemen

Iran ta yi tir da Allah wadai da kakkausan lafazi da harin Amurka na baya baya nan kan tashar mai ta kasar Yemen, wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane tare da lalata dukiya mai yawa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya kira harin da Amurka ta kai a matsayin keta kundin tsarin […]
Sheikh Qassem ya yi fatali da kiraye-kirayen kwance damarar Hezbollah

Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya yi Allah wadai da kalaman da kiraye kirayen da ake na “kwance damarar” kungiyar Hizbullah, yana mai kiransa da cewa wani yunkuri ne na raunata kasar Lebanon da kuma ci gaba da fadada manufofin Tel Aviv. Sheikh Naim Qassem ya bayyya hakan ne a wani jawani da […]
Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu

Kasashen Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu domin cin moriyar juna a matsayinsu na makobta. Wannan bayyanin ya fito bayan tattaunawa data wakana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu a birnin Yamai bayan kwashe watanni ana takaddama. Yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai Nijar an gudanar da wani […]
Amurka za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi

Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni. Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki, […]